(ABNA24.com) Kungiyar ta ce kimanin ma’aikatan ofisoshin jakancin haramtacciyar kasar 90 ne suka sanar da shirinsu na shiga cikin wannan yajin aiki, bayan da suka zargi gwamnatin Netanyahu da mayar da jami’an diflomasiyarta saniyar ware a yayin gudanar da wasu al’amuranta a kasashen waje.
Har ila yau kungiyar ma’aikatan ofisoshin jakadancin Isra’ila sun zargi gwamnatinsu da rage kudaden da take bayarwa ga ma’aikatar harakokin waje.
Sanarwa ta kara da cewa matukar dai gwamnatin Netanyahu ta ci gaba da wannan siyasa to za ta rusa bangaren siyasar Isra’ila kuma ta zamanto gwamnati daya tilo a duniya wadda ba ta aiki da bangaren diflomasiyya.
A wannan Litinin ne Jakadun Isra’ilan dake kasashen Afirka za su gudanar da nasu yajin aiki, inda a gobe Talata na kasashen Turai za su gudanar da na su yajin aikin, ranar Laraba ma na kasashen arewacin Amurka ne za su shiga na su yajin aikin, sai kuma ranar Alhamis ga ma’aikatan yankin Asiya.
/129
23 Yuli 2019 - 04:29
Lambar labari: 963587
Kungiyar ma’aikatan diflomasiyar Isra’ila sun sanar a jiya Lahadi cewa a mako mai zuwa za su tsunduma cikin yajin aiki na nuna adawa da siyasar gwamnatin Benjamin Netanyahu.